Majalisa ta janye dukkan tuhumar da ta ke yi wa tsohon mataimakin gwamnan Kano Aminu Abdussalam Gwarzo
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Majalisar dokokin jihar Kano ta janye dukkanin tuhumar da ta ke yi wa tsohon mataimakin Gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo.
A yayin zaman majalisar na yau Talata 7 ga watan Afrilu, 2026, shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Husaini Dala, ya ce sun ɗauki wannan matakin ne bayan da Gwarzo ya bayyana saukar sa daga kujerar ta sa bisa raɗin kansa.
Wakilinmu na majalisar Sunusi Shu'aibu Musa ya ruwaito cewa, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Kiru, Tasi'u Kiru, ya sanar da ficewar sa daga jam'iyyar NNPP zuwa ADC.



