Gwamnan Kano ya zargi tsohon mataimakin sa da yunƙurin damalmala lamura don ya ɗare kujerar sa

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya zargi tsohon mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, da yunƙurin kawar da shi daga kujerar mulki, domin ya ɗare kujerar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a yayin ganawar sa da mawaƙansa. (mawallafa Abba gida gida).
Kazalika, Gwamnan ya kuma zargi tsohon mataimakin nasa da yi masa bita da ƙulli iri-iri inda ya damalmala alʼamura, yana mai cewa Gwarzo ya yi hakan ne don ya samu ya kawar da shi shi kuma ya ɗare kujerar.
Gwamnan ya ci gaba da cewa, "Yau gashi baya nan ya tafi mu kuma muna nan har zuwa waʼadin da Allah ya ɗibar mana, in ji Abba.”
Gwamnan ya kuma bayyana cewa, bayan tafiyar tsohon mataimaki na ga shi nan mutane masu biyayya suna ta rububin kujerar, kamar yadda kafar Arewa updates ta ruwaito.
Kazalika Gwamnan ya ƙalubalanci tsohon mai gidansa wato Engr. Rabiʼu Musa Kwankwaso da cewa, shin me ya sa ba za a bai wa shi mataimakin Gwamnan da ya tafi saboda kwaɗayin kujerar gwamna takara ba?
Sai dai zuwa wannan lokaci ba a ji martanin mataimakin gwamnan a kan zargin ba, amma da zarar ya magantu za a ji martanin nasa.



