An rantsar da Ali Musa Hardwoker a matsayin halartaccen shugaban karamar hukumar Kumbotso a Kano
0 views

Hukumar Zabe ta jihar Kano KANSIEC ta rantsar da Hon. Ali Musa Ɗanmaliki, (Hardwoker) a matsayin halartaccen shugaban karamar hukumar Kumbotso a Kano.
Hukumar ta rantsar da Hardwoker, ne a yau Talata, bayan sauke Abdullahi Ghali Basaf daga shugaban karamar hukumar Kumbotso, yayin da aka maye gurbin sa da Ali Musa.
Bayan hukuncin babbar kotun jihar Kano na sauke Ghali Abdullahi Basaf daga shugabancin ƙaramar hukumar Kumbotso, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano ta mika shedar lashe zaɓe ga Hon. Ali Musa Hardworker.
Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Kano, KANSIEC, Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya mika shedar a yau Talata a gidan gwamnatin jihar Kano.



