Koma Labarai
Siyasa

Gwamnan Kano ya rantsar da Hardworker a matsayin sabon shugaban karamar hukumar Kumbotso

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnan Kano ya rantsar da Hardworker a matsayin sabon shugaban karamar hukumar Kumbotso

Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da Hon. Ali Musa Hardworker, a matsayin sabon shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso, biyo bayan hukuncin kotu da ya tabbatar da zaɓen sa.

Wannan na cikin wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba 25 ga watan Maris, 2026.

Sanarwar ta ce an gudanar da rantsuwar ne a ranar Talata 24 ga Maris, 2026 a Fadar Gwamnatin Kano.

A yayin taron rantsar da shi, Gwamna Yusuf ya buƙaci sabon shugaban da ya gudanar da aikinsa cikin gaskiya da riƙon amana, tare da jaddada muhimmancin shugabanci na gari a matakin ƙananan hukumomi.

Sanarwar ta kuma ce, nasarar gwamnati tana dogara ne da yadda shugabanni ke gudanar da ayyukansu a matakin kasa.

Gwamnan ya kuma buƙaci Hardworker, da ya fifita buƙatun al’ummar ƙaramar hukumar Kumbotso, tare da kuma tabbatar da ci gaba mai ma’ana a dukkan unguwanni.

A nasa bangaren, Hon. Ali Musa Hardworker, ya gode wa gwamnan da al’ummar karamar hukumar bisa amincewar da suka nuna masa, tare da yin alƙawarin yin aiki tuƙuru, domin inganta rayuwar jama’a.

Rantsar da Ali Musa, na zuwa ne biyo bayan hukuncin babbar kotun Kano da ta soke zaben tsohon shugaban karamar hukumar Kumbotso Abdullahi Ghali Basaf, tare da tabbatar da Ali Musa Hardwoker, a matsayin shugaban ƙaramar hukumar.

Ready to PlayDala FM88.5 FM