Gwamnan Legas ya amince da mataimakinsa Obafemi a matsayin ɗan takarar gwamna a zaɓen 2027
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya amince da mataimakinsa Obafemi Hamzat a matsayin ɗan takarar gwamna a zaɓen 2027, da ke tafe.
Wannan ya biyo bayan tattauna wa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, inda suka nuna goyon baya ga takarar Obafemi Hamzat a zaɓen 2027.
Wannan na zuwa ne yayin da zaɓen 2027, ke ƙara gabatowa, inda masu sha'awar tsayawa takara ke ta nuna sha'awar su.



