Koma Labarai
Labarai

Gwamnatin tarayya ta buɗe shafin tallafin karatu na PTDF ga ɗaliban Injiniya

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnatin tarayya ta buɗe shafin tallafin karatu na PTDF ga ɗaliban Injiniya

Hukumar Bunƙasa Fasahar Man Fetur (PTDF) ta sanar da buɗe shafin neman tallafin karatu na shekarar 2025/2026 ga ɗaliban da ke karatun aikin injiniya da sauran fannoni masu alaƙa da harkar man fetur a jami’o’in Najeriya.

Hukumar ta buɗe shafin ne a ranar Litinin, 20 ga watan Afrilu, 2026, inda aka tsara rufe karɓar rejista a ranar Juma’a, 29 ga watan Mayu, 2026.

A cewar wata sanarwa da hukumar ta fitar, wannan tallafi ya shafi ɗaliban da ke matakin digiri na farko (Undergraduate) da kuma masu neman digiri na biyu da na uku (Postgraduate). Manufar shirin ita ce ƙarfafa kishin gida da samar da kwararru a fannin fasaha don rage dogaro da masana daga ƙasashen waje.

Masu sha’awa za su iya rejista ta shafin: https://scholarship.ptdf.gov.ng

Hukumar PTDF ta fitar da matakai guda goma da ya kamata masu nema su bi:

1. Buɗe Akawun: Ziyarci shafin tallafin, sannan ka samar da akawun ta hanyar shigar da bayananka. Za a turo maka sako ta imel don tabbatarwa.

2. Shiga Shafin (Login): Yi amfani da imel da kalmar sirri (password) don shiga shafin akawun dinka.

3. Tabbatar da Lambar NIN: Wajibi ne mai nema ya tabbatar da lambar sa ta shaidar ɗan ƙasa (NIN). Hukumar ta yi kashedin cewa idan aka samu matsala wajen tantancewa, kada a riƙa maimaitawa akai-akai don gudun asarar kuɗi; kamata ya yi a tuntuɓi sashen taimako.

4. Yarda da Sharuɗɗa: Dole ne ka karanta sannan ka amince da sharuɗɗan shirin kafin ka ci gaba.

5. Cike Fom: Shigar da dukkan bayanan da ake buƙata cikin kwarewa da gaskiya.

6. Zaɓar Karatu da Jami’a: Zaɓi jami’o’i da darusan da kake son karantawa (na farko, na biyu, da na uku). Masu neman digiri na biyu da na uku za su loda takardar bayyana manufar karatu (Statement of Purpose) ko shawarar bincike (Research Proposal).

7. Ɗora Takardu: Ana buƙatar takardar shaidar karatu, takardar haihuwa, da ta ɗan ƙasa da jiha. Dole takardun su kasance cikin tsarin PDF kuma girmansu bai fi 300KB ba.

8. Ƙarin Takardu: Za ka iya loda takardun kasancewa dan daya daga ƙungiyoyin kwararru idan kana da su.

9. Duba Bayanan da aka shigar: Tabbatar ka duba dukkan bayanan da ka shigar don gyara kura-kurai kafin ka tura.

10. Tura bayanai: Da zaran ka tura, ba za ka iya sake gyara komai ba. Don haka, a tabbatar komai ya kammala kafin dannawa a tura.

Wannan tallafi na cikin gida (In-country scholarship) ya bambanta da wanda ake fita ƙasashen waje don yi. Tallafin yana rufe kuɗin makaranta, kuɗin alawus na wata-wata, da kuma samar da kayan karatu ga ɗaliban da suka yi nasara bisa cancanta.

Hukumar ta jaddada cewa wannan yunkuri wani ɓangare ne na dabarun gwamnatin tarayya na haɓaka jarin bil-adama a fannin makamashi na ƙasa.

Ready to PlayDala FM88.5 FM