Koma Labarai
Labarai

Majalisa ta kafa kwamitin tantance Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Majalisa ta kafa kwamitin tantance Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta kafa kwamiti bisa jagorancin mataimakin shugaban majalisar, Muhammad Bello, da zai gayyaci Murtala Sule Garo domin tantance shi don zama mataimakin gwamnan Kano.

Wannan na zuwa ne a yayin zaman majalisar dokokin Kano, da ya gudana a ranar Laraba 22 ga watan Afrilu, 2026.

Wakilinmu na Majalisar dokokin jihar Kano, Sunusi Shu'aibu Musa ya ruwaito cewa, kwamitin zai bayar da rahoton sa a gaban majalisar a ranar Litinin mai zuwa.

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ne dai ya miƙa sunan Sule Garo, a matsayin wanda za ta tantance a matsayin mataimakin gwamnan Jihar Kano.

Ready to PlayDala FM88.5 FM