Trump ya ce za su kawo ƙarshen yaƙin Iran ko da yarjejeniya ko babu

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump ya nuna cewa yana son ya rage hare-haren da ake kai wa Iran, yana mai alƙawarin cewa yaƙin zai zo karshe a cikin mako biyu ko uku masu zuwa, ko da an cimma yarjejeniya ko ba a cimma hakan ba.
Trump ya kuma ce yanzu Iran tana da sababbin shugabanni waɗanda suka fi sauƙin samu, ba masu tsattsauran ra'ayi ba kuma waɗanda suka fi magabatansu hankali.
A cewar sa, "Gwamnatin Amurka ta cimma burinta, duk da cewa ba ta iya ƙwace mashigar Hormuz ba daga hannun Iran; yiyuwar ci gaba da ƙarancin mai, farashin ɗanyen man ya ƙara tashi a yau Laraba 1 ga watan Apir, 2026."
Sai dai kuma, Trump ya ce nan gaba kaɗan farashin zai sauka. A yau zai gabatar da jawabi ga al'ummar kasar ta Amurka ta talabijin, kamar yadda kafar BBC ta ruwaito.



