An naɗa DCP Anthony Okon Placid a matsayin sabon Kakakin Ƴan Sandan Najeriya.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu, ya amince da naɗin DCP Anthony Okon Placid, a matsayin sabon Jami'in Hulɗa da Jama'a na Rundunar ta ƙasa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar mai barin gado ACP Benjamin Hundeyin ya fitar a ranar Lahadi 8 ga watan Maris, 2026.
Sanawar ta kuma ce sabon kakakin rundunar DCP Anthony Okon Placid, ƙwararren jami'i ne, wanda ke da gogewa a fannin gudanarwa, da ayyuka na musamman, leken asiri da kuma samar da zaman lafiya a duniya.
DCP Anthony Okon Placid, mai shekaru 56, ya kasance ɗan asalin jihar Akwa Ibom.

