Koma Labarai
Ƙetare

A karon farko: Iran da Saudiyya sun tattauna tun bayan fara yaƙin Gabas ta Tsakiya

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
A karon farko: Iran da Saudiyya sun tattauna tun bayan fara yaƙin Gabas ta Tsakiya

Rahotanni sun bayyana cewa, Ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan Al Saud, ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Iran, Abbas Araqchi, a karon farko tun bayan ɓarkewar yaƙi da hare‑haren Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta bayyana a shafin ta na X cewa, ministocin biyu sun tattauna kan sabbin abubuwan da suka faru a yankin, tare da bincikar hanyoyin rage tashin hankali don dawo da tsaro da kwanciyar hankali a yankin

Majiyoyi sun bayyana cewa wannan shi ne mataki na farko na hulɗa kai tsaye a tsakanin ƙasashen biyu a cikin wannan rikici da ake yi, kamar yadda kafar BBC ta ruwaito.

Ready to PlayDala FM88.5 FM