Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta buƙaci a kawo mata littattafan da Abduljabbar ya gabatar a matsayin shaidar kariya a kotun kofar kudu, Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta buƙaci a kawo mata littattafan da Abduljabbar ya gabatar a matsayin shaidar kariya a kotun kofar kudu, Kano.

Babbar Kotun jahar Kano, ɓangaren ɗaukaka ƙara ta saurari ɗaukaka ƙarar da Mallam Abduljabbar Nasir Kabara ya shigar yana ƙalubalantar hukunci kisa da kotun shari'ar Muslunci ta kofar kudu a Kano, ta yanke masa bisa samun sa da laifin ɓatanci ga fiyayyen halitta.

A zaman kotun na ranar Litinin 29 ga Yuni, 2026, lauyoyin mai daukaka kara da na gwamnati sun bayyana hujjojin su, inda masu ɗaukaka ƙarar su ka roƙi kotun da ta wanke malamin ta kuma sallame shi.

Sai dai ɓangaren masu karbar ɗaukaka ƙara sun roƙi kotun da ta tabbatar da hukuncin kotun farko.

Mai shari'a Nasir Saminu ya bukaci a gabatar masa da wasu littattafai da aka gabatar a kotun farko.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, nan gaba kadan kotun za ta bayyana ranar da za ta bayyana matsayarta a kan shari'ar.

Ready to PlayDala FM88.5 FM