Koma Labarai
Labarai

Hajjin 2027: Saudiyya ta ƙara wa Najeriya kujeru 10,000.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hajjin 2027: Saudiyya ta ƙara wa Najeriya kujeru 10,000.

Hukumar kula da aikin hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ce Saudiyya ta ƙara wa Najeriya kujerun aikin Hajjin 2027 da 10,000, lamarin da ya ɗaga adadin kujerun ƙasar daga 50,000 zuwa 60,000.

Wannan na cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai na hukumar, Shafii Mohammed, ya fitar ranar Alhamis 1 ga watan Oktoba, 2026.

A cewar hukumar, an ware kujeru 7,500 daga cikin ƙarin adadin ga hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi, yayin da aka bai wa kamfanonin shirya aikin Hajji guda bakwai kujeru 2,500.

Sanarwar ta ce, Shugaban NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya gode wa gwamnatin Najeriya da hukumomin Saudiyya, bisa ƙarin kujerun, kuma za a rarraba su cikin gaskiya da bin dokokin Najeriya da Saudiyya.

Hukumar ta ce ƙarin kujerun ya biyo bayan tattaunawar diflomasiyya a tsakanin Najeriya da ƙasar Saudiyya.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM