Za a hukunta duk lauyan gwamnati da bai fito aiki ba - Ma'aikatar shari'a a Kano.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Hukumar gudanarwa ta ma'aikatar shari'a ta jihar Kano, ta bayyana cewar za a hukunta duk lauyan da bai fito aiki a gobe Laraba ba.
Hakan na cikin sanarwar da hukumar ta fitar a cikin daren Talata 10 ga watan Maris, 2026.
Hukumar gudanarwar ta bayyana cewar tun daga kan daraktoci har zuwa kan ƙananun ma'aikata ba a ɗauke wa kowa zuwa aiki ba.
Wakilin Dala FM Kano, Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, hukumar ta kuma ce bijirewa sanarwar dai-dai ta ke da saɓawa dokar ɗauka da ladabtar da ma'akaci.
Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ƙungiyar lauyoyin gwamnati reshen jihar Kano, ke shirin shiga yajin aikin sai baba ta gani, sakamakon jan ƙafa a kan haƙƙoƙinsu da suka maƙale a ma'aikatar.

