Gwamnan Kano ya tura wa majalisar dokoki sunayen mutane 6 da za a naɗa su kwamishinoni a jihar.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Majalisar dokokin Kano ta karɓi sunayen mutane shida da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin naɗa su a matsayin Kwamishinoni, kuma manbobi a kwamitin zartarwa na jihar.
Da yake karanto wasikar a zaman majalisar na yau Laraba, Kakakin majalisar, Jibril Ismail Falgore, ya ce daga cikin sunayen mutum shida da aka aike, sun haɗar da Air Commado Salisu Yusha'u mai ritaya, da Farfesa Sani Lawan da kuma Hon. Muntari Ishaq.
Ragowar sun haɗar da Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa da Hon. Idris Garba Mustapha sai Ibrahim Namadi Dala, kamar yadda wakilinmu Sunusi Shu'aibu Musa ya ruwaito.



