Koma Labarai
Labarai

Ɗaliba ta roƙi Gwamnatin Kano da ta sa baki kan tsare wani ɗalibi da aka yi a jihar

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ɗaliba ta roƙi Gwamnatin Kano da ta sa baki kan tsare wani ɗalibi da aka yi a jihar

Wata ɗalibar digirin-digirgir (PhD) a Jami’ar Bedfordshire da ke Birtaniya, Sa’adatu Baba Ahmad, ta roƙi Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya sa baki kan batun tsare wani matashin ɗalibi wanda ake kira da Aiha Ƙofar Nassarawa, da ake zargin an tsare shi sakamakon wata takaddama da ta shafi ra’ayinsa na siyasa.

Ta ce tsarewar na iya kawo cikas ga karatunsa, musamman kasancewarsa yana rasa darussa da jarabawar gwaji a makaranta.

A wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ta aika wa gwamnan, Sa’adatu ta yi kira da a duba yiwuwar amfani da wasu hanyoyin gyaran hali da hukunci, kamar gargadi, belin kotu ko hidimar al’umma, idan doka ta ba da damar hakan.

Ta kuma jaddada muhimmancin kare haƙƙin matasa na bayyana ra’ayoyinsu cikin lumana, tare da tabbatar da cewa duk wani mataki da aka ɗauka a kansu ya kasance bisa tanadin doka.

Sa’adatu ta ce, duk da cewa ba ta da wata alaƙa ta musamman da ɗalibi Aiha, ta damu da halin da yake ciki ne saboda kasancewarsa matashi mai karatu, kamar yadda kafar Daily Nigerian ta ruwaito.

Ta roƙi gwamnan da ya yi amfani da matsayinsa wajen duba lamarin cikin tausayi da hangen nesa, tana mai cewa kare makomar matasa da ba su damar ci gaba da karatu na daga cikin hanyoyin gina al’umma mai inganci.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM