Koma Labarai
Labarai

Tirƙashi: Tawagar likitoci sun ciro wuƙaƙe samfurin Zabira guda 40 daga cikin wani ɗan sanda a India.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Tirƙashi: Tawagar likitoci sun ciro wuƙaƙe samfurin Zabira guda 40 daga cikin wani ɗan sanda a India.

Wani ɗan sanda mai shekaru 42 a Indiya, ya kai kansa asibiti saboda matsanancin ciwon ciki da ke damunsa, inda da farko likitoci suka yi zargin cewa, wani abu ne ke damunsa a ciki.

Sai dai bayan an yi masa gwaje-gwaje da hoton CT, sai aka gano wani abu mai ban mamaki: wuƙaƙe samfurin zabira guda 28 ne suke cikin cikinsa! An kai shi ɗakin tiyata, inda likitoci suka fara cire su ɗaya bayan ɗaya.

Bayan an cire wuƙaƙe 28 ɗin, likitocin suka sake bincika cikinsa kafin su rufe shi, sai suka gano wasu wuƙaƙe zabira 12. Hakan ya sa adadin ya kai zabirori gida 40, kuma an shafe kusan sa'o'i biyar ana aikin tiyatar. Wasu daga cikin wuƙaƙen a buɗe suke, wasu a naɗe, wasu kuma sun lalace saboda tsatsa.

Mutumin ya shaida wa likitoci cewa, ya fara haɗiye wuƙaƙen ne a watan Yunin 2016, kuma daga baya abin ya koma ɗabi'a. Ya kuma ce, ya na jin wani ƙarfi na ruhaniya ne ke tura shi yin hakan. Likitoci sun yi zargin cewa, akwai wata matsalar ɗabi'a ko ta lafiyar ƙwaƙwalwa da ke da alaƙa da wannan hali, kuma sun shirya masa kulawar ƙwararru.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM