Koma Labarai
Labarai

Jarumi a masana'antar Kannywood Adam A Zango, ya shirya tafiya hutun Film na watanni uku.

Hassan Mamuda Yau 0 views
Jarumi a masana'antar Kannywood Adam A Zango, ya shirya tafiya hutun Film na watanni uku.

Jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A Zango, ya shirya tafiya hutun Film domin samun dama wajen kula da lafiyar sa.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Adam A Zango ya sanar da hakan ne a shafin sa na sada zumunta ranar Juma'a 09 ga watan Oktoba, 2026.

A rubutun da ya wallafa ya ce, "Ina mai sanar da abokan sana'a ta cewa, zan tafi hutun watanni uku, daga ranar 10/11/2026 zuwa 10/02/2027 sakamakon duba lafiyata don haka ina buƙatar samun cikakken hutu da kulawa," in ji shi.

A cewar jarumin, yana fatan al'umma za su fahimci halin da yake ciki, tare da ba shi haɗin kai da goyon baya a wannan lokaci.

Ya kuma yi roƙon Allah maɗaukakin Sarki ya ba shi lafiya mai ɗorewa, tare da dukkanin musulmai da suke jinya.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM