Kwamishinan ƴan sandan Kano, ya nemi gidajen rediyo su rinƙa tantance masu magana kan siyasa.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta nemi gidajen rediyo da su dinga tantance irin mutanen da za su rinƙa basu damar magana a rediyo da nufin sauƙaƙa rigingimun da ke biyo baya ta sanadiyyar rikicin siyasa.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar aiki da kungiyar ƴan jaridun da ke ɗakko rahotannin kotu da ƴansanda na gidajen rediyon Kano, National Association of Crime Correspondents Kano State Chapter, suka kai masa ziyarar girmamawa da ƙara jaddada alaƙar aiki a yammacin Talata 8 ga watan Satumba, 2026.
Kwamishinan ya ƙara da cewa, ƴan jaridu nada muhimmiyar rawar da suke takawa wajan tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano, sai dai damar da wasu gidajen rediyon ke baiwa wasu da sunan ƴan siyasa ba komai suke ba, illa dagula al'amura da barazana ga zaman lafiya.
A cewar sa, "Ƴan jarida suna da rawar da za su taka wajan taƙaita hakan koma hanawa domin samun tabbataccen zaman lafiya a jihar Kano," in ji shi.
Da yake nasa jawabin mataimakin shugaban ƙungiyar ta National Association of Crime Correspondents Kano State Chapter, Yusuf Nadabo Isma'il na Dala FM Kano, ya ce ziyarar na da alaƙa da sake Jaddada alaƙar aiki domin samun nasarar da ake fata.
Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Nadabo ya ƙara da cewar, alaƙar aiki tsakanin ƴan jarida da ƴansanda a jihar Kano abace da ta daɗe, kuma aiki tare zai taimaka wajan cigaban zaman lafiya da tabbatuwar al'amuran a jihar Kano.



