Ƴansandan Kano sun gayyaci ɗan takarar NDC, Aminu Warkal kan zargin fito da bindiga a taron siyasa

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta gayyaci ɗan takarar Majalisar Jiha mai wakiltar ƙaramar hukumar Gwale, a jam'iyyar NDC, Aminu Abdullahi Warkal, domin amsa tambayoyi kan wani bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta, wanda a ciki aka ganshi yana fito da bindiga a wani taron siyasa.
Rundunar ta ce ta gano bidiyon ne yayin da take gudanar da sintirin sa ido a kafafen intanet, inda aka ga Warkal yana nuna wata bindiga da ake kyautata zaton cewa Pump Action Rifle ce.
Ƴan sandan sun ce idan bincike ya tabbatar da zargin, nuna bindigar ba bisa ka’ida ba na iya zama karya dokar mallaka da amfani da makami, kuma hakan na iya tayar da hankalin jama’a tare da barazana ga zaman lafiya.
Sanarwar da kakain rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, rundunar tace Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori ne ya bada umarnin gayyatar Warkal kuma yanzu haka yana ofishin rundunar inda yake amsa tambayoyi.



