Rundunar Anti-Phone Snatching force ta kama Ali Baban Jakai, da ake zargi da jagorantar masu sanen waya a kasuwar Bata, Kano.

Rundunar tsaro ta Anti-illicit drugs and Phone Snaching force ta jihar Kano, ta kama wani matashi da ake kira da Ali Baban Jakai, bisa zargin sa da jagorantar wasu matasa wajen yi wa mutane sanen wayoyi da kuɗaɗe a Bata zuwa Ƴan Kura.
Kwamandan rundunar tsaron da ke yaƙi da faɗan daba, ƙwacen waya da daƙile sha da dillancin kayan maye, CMD Nura Salisu Sharaɗa, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano, ranar Lahadi 08 ga Nuwamba, 2026.
Ya ce kama Ali Baban Jakai, ya biyo bayan kama wasu matasa su goma waɗanda aka yi zargin suna sanen wayoyi, da kuɗaɗen mutane a kasuwar Bata zuwa Ƴan Kura.
A cewar sa, "Dama mun daɗe mu na neman Ali Baban Jakai, ruwa a jallo, bisa zargin sa da jagorantar wasu matasa suna yi wa mutane sanen wayoyi da kuɗaɗe a kasuwanni, sai kuma gashi matasan da muka kama suka rinƙa ambata sunan Baban Jakai, da cewar mai gidan su ne," in ji Nura.
Ya kuma ƙara da cewa, bayan da ya tura jami'an sa masu yaƙi da satar waya na "Operation Phone Snaching" suka bazama inda suka kamo Ali Baban Jakai, a cikin Sabon gari, zagaye da wasu mata, da kuma Giya, a gefen sa.
Da yake bayyana badamar sa, matashi Ali Baban Jakai, ya ce abaya ya taɓa sanen wayoyi da kuɗaɗen jama'a, amma dai a yanzu ya daina, kasancewar ya ga ba hanya ce mai ɓullewa ba.
Ya ce kafin ya daina, ya shafe sama da shekaru shida yana harkar sanen wayoyi da kudaɗe, domin hakan ne ya sa a yanzu idan mutum ya ce an sace wayar wayar a kasuwar Bata, ko Ƴan Kura, yakan iya sanin wanda ya saci wayar ya kuma sa a dawo da ita.
Ali Baban Jakai, ya kuma musanta zargin da matasan da aka kama suka yi, na cewar shi ne mai gidan su, amma dai ya ce ya san su.
Sai dai daga bisani, Kwamandan rundunar tsaron ta Anti-illicit drugs and Phone Snaching force a Kano, Nura Salisu Sharaɗa, ya ce da zarar sun kammala bincike za su miƙa matashi Ali Baban Jakai, inda ya dace domin ɗaukar matakin da ya dace a kan sa.



