Ƴan sandan Kano sun cafke matashi Ta'ambo, da ake zargi da fice wajen faɗan daba da fashi da makami.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Umar Usman, wanda aka fi sani da ‘Ta’ambo’, mai shekaru 25, bisa zargin jagorantar ayyukan daba da fashi da makami a yankin Rimin Kebe da kewaye.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026.
Ya ce jami’an rundunar sun kama wanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 8:40 na dare, bayan samun bayanan sirri da kuma sa ido na tsawon makonni a kan sa.
Sanarwar ta ce ana zargin Ta’ambo da jagorantar ayyukan daba, da kwacen wayoyin hannu da kai hare-hare kan jami’an tsaro a Rimin Kebe, yankin Ramin Research da kuma kusa da Asibitin Galula.
Rundunar ta ce a halin yanzu matashin yana hannun ’yan sanda, ana ci gaba da bincike da ƙoƙarin cafke sauran waɗanda ake zargi da hannu a ayyukan.
Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin kama matashin.
Bakori ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa rundunar bayanan sirri, domin kawo ƙarshen daba da sauran miyagun laifuffuka a faɗin jihar Kano.



