Bincike: Gwamnan Kano Abba, ya nemi a sauya Kwamishinan ƴansanda da DPO 18 gabanin zaɓen 2027

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya nemi a sauya wurin aiki na Kwamishinan ’yansandan jihar, CP Ibrahim Bakori, tare da sauya jami’an ’yan sanda 18 masu kula da ofisoshin ‘yansanda (DPOs) a wasu muhimman sassan jihar gabanin babban zaɓen ranar 16 ga Janairun 2027.
Wata majiya ta shaida wa jaridar Daily Nigerian cewa gwamnan ya gabatar da sunan sabon kwamishinan ’yansanda, CP Mohammed Yusuf Adamu, wanda aka ƙara wa girma kwanan nan, domin maye gurbin Bakori.
Majiyoyin sun ce ana sa ran sabon kwamishinan zai fara aiki a kowane lokaci daga yanzu.
Rahoton ya ce matakin ya biyo bayan rashin jituwa tsakanin gwamnan da kwamishinan ’yansandan kan sauye-sauyen wuraren aikin wasu manyan jami’an rundunar a jihar.
A cewar majiyoyin, CP Bakori ya sauya wasu DPOs, inda ya maye gurbinsu da manyan jami’ai bisa la’akari da girma da ƙwarewa a aikin.
Wata majiya ta ce akwai jami’an ’yansanda masu mukamin CSP da dama da ke zaune ba tare da aiki na musamman ba a hedikwatar rundunar, yayin da ƙananansu ke jagorantar sassan ‘yan sanda.
Majiyar ta ƙara da cewa wannan mataki bai yi wa gwamnan daɗi ba, wanda ya nemi a sauya shawarar daga sama.
Rahoton ya kuma bayyana cewa Sufeto-Janar na ’yansanda ya sauya wuraren aikin DPOs 18 daga Kano zuwa wasu jihohi, ciki har da Yobe, Gombe, Kebbi, Sokoto, Zamfara da Katsina.
Sai dai, a wata takarda mai ɗauke da ranar 15 ga Oktoba, 2026, hedikwatar rundunar ’yansandan ta bayar da umarnin mayar da wasu jami’an da Bakori ya sauya zuwa tsoffin wuraren aikinsu, tare da yin wasu sabbin nade-nade da ake zargin sun yi daidai da buƙatun gwamnan.
Ofisishin da abin ya shafa sun haɗa da Fagge, Gwale, Ungogo, Kumbotso, Sharada, Bompai da Bichi, da sauransu.
Wannan lamari ya haifar da tambayoyi kan yiwuwar katsalandan na siyasa a harkokin naɗe-naɗen jami’an ’yansanda da kuma ƙoƙarin samun tasiri kan tsarin tsaro a jihar gabanin zaɓen 2027.
Jaridar ta rawaito cewa a lokacin shirye-shiryen zaɓen 2023, ta taɓo wasu zarge-zargen shirye-shiryen tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, na neman naɗa kwamishinonin ’yan sanda masu biyayya gare shi domin yin tasiri kan zaɓen.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan ƙasa, Anietie Iniedu, domin jin ta bakinsa, bai amsa kiran waya ko saƙon da aka aika masa ba.
Sai dai kakakin gwamnan Kano, Mustapha Mohammed, ya ce bashi da masaniya a kan batun.
“Ban san da wannan batu ba. Ba ni da irin wannan bayanin, kuma ba zan iya yin tsokaci a kai ba,” in ji shi.



