Koma Labarai
Tsaro

Ƴan sandan Kano sun kama matasa 2 kan zargin yunƙurin sace Dagacin Ɓangare da ke Gezawa.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ƴan sandan Kano sun kama matasa 2 kan zargin yunƙurin sace Dagacin Ɓangare da ke Gezawa.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama matasa biyu masu shekaru 20 kowannensu, kan zargin haɗa baki da yunƙurin sace Dagacin Garin Bangare, Malam Idris, a Karamar Hukumar Gezawa ta Jihar Kano.

Wannan na cikin sanarwar da Kakakin Rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Laraba, 28 ga Oktoba, 2026.

Sanarwar ta ce dagacin ya karɓi kiran waya daga wani mutum da bai sani ba a ranar 24 ga Oktoba, 2026, da misalin ƙarfe 9:33 na dare, inda aka yi masa barazanar yin garkuwa da shi, kafin ya kai ƙorafin ga ’Yan Sanda a ranar 26 ga Oktoban 2026.

Rundunar ta ce, bayan samun ƙorafin, jami’an ’Yan Sandan Gezawa sun gudanar da bincike ta hanyar amfani da bayanan sirri, wanda ya kai ga kama Aliyu Naziru Garba da Bashir Alhasan, masu shekaru 20 kowannensu, kamar yadda kafar Arewa update ta ruwaito.

Ƴan sandan sun ce, matasan sun amsa zarge-zargen da ake yi musu yayin bincike, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala binciken da ake gudanarwa.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM