Koma Labarai
Tsaro

Zaɓen 2027: Matasa ku guji shiga bangar siyasa - Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewa

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Zaɓen 2027: Matasa ku guji shiga bangar siyasa - Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewa

Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewacin Najeriya, ta buƙaci matasa da su ƙauracewa shiga bangar siyasa a yaƙin neman babban zaɓen 2027, domin tsira da mutuncin su.

Shugaban Ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Muhammad Tijjani Ɗorayi (MTD) ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Dala FM Kano, ranar Alhamis 29 ga watan Oktoba, 2026.

Ya ce bai kamata matasan su rinƙa shiga bangar siyasa ba, domin gujewa fuskantar matsala a rayuwar su ta yau da kullum.

A cewar sa, "Matasa duk ɗan siyasar da ya ce muku ga makamai, ko ƙwayoyi ku yi masa rakiya a lokacin yaƙin neman zaɓe, ku faɗa masa ya fito da ƴaƴan sa ku je tare tunda dai mutumci bai fi mutunci ba," in ji shi.

MTD ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi da su tsawatarwa ƴan siyasa kan gujewa sanya matasa shiga bangar siyasa, domin tseratar da mutuncin su.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da babban zaɓen shekarar 2027, ke ƙara gabatowa.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM