Koma Labarai
Tsaro

Ƴan Sandan Zamfara sun cafke ɗan agajin Izala da ake zargin ya yi bidiyon neman a kai hari Jahohin Filato, Enugu.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ƴan Sandan Zamfara sun cafke ɗan agajin Izala da ake zargin ya yi bidiyon neman a kai hari Jahohin Filato, Enugu.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta kama dan agajin Izala da ake zargin yayi bidiyon neman a kai hari jihohin Enugu da Filato.

Kafar Arewa Updates ta rawaito cewa, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, A. M. Bello, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a ranar Talata, 27 ga Oktoba, 2026.

Ya ce, bidiyon da aka ɗauka ranar Juma'a, 23 ga Oktoba, 2026, ya nuna matashin sanye da kayan agajin Izala tare da ɗaliban makarantun Islamiyya, inda ake zarginsa da rera waƙar da ke ɗauke da kalaman daukar bindigogi domin kai hari kan Kiristoci a Enugu da Jos.

Rundunar ta bayyana sunan wanda ake zargin da Umar Ibrahim Gandi Maradun, inda ta ce shugabannin ƙungiyar Izala sun nesanta kansu daga kalaman da ake zarginsa da yi, tare da kama shi da miƙa shi ga ’yan sanda domin bincike.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM