Rundunar Kossap ta cafke matashi bisa zargin satar wayar abokansa da sayar da kayan maye a wajen Maulidi a Kano.

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba, ƙwacen waya da daƙile sha da dillancin kayan maye, ta Anti-illicit drugs/Phone Snaching force a Kano, ta cafke matashi Ibrahim Dauda, mai shekaru 20, bisa zargin sa da laifin satar wayar abokan sa.
Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Matashin mazaunin unguwar Bubbugaje a Kano, rundunar ta kama shi ne bisa cin amanar abokansa, inda aka yi zargin ya sace wayar abokan nasa lokacin da suke zaune a unguwar su.
Kwamandan rundunar tsaron ta Anti-illicit drugs/Phone Snaching force a Kano, CMD Nura Salisu Sharaɗa, ya ce bayan da suka samu bayanan sirri kan abinda matashin ya yi ne ya tura jami'ansu suka kamo shi.
A cewar sa, "Binciken mu na farko ya gano cewa, matashin ya ɗauke wayar ne bayan da abokan sa suka ajiye har ya je ya sayar da ita, amma daga bisani an gano wayar," in ji Nura Sharaɗa.
Ya kuma ce binciken rundunar ya gano cewa, matashin yana zuwa guraren da ake tarukan addini, kamar Maulidi, da sauransu, yana sayar da kayan shaye-shaye domin ya samu kuɗin kashewa.
Sai dai matashin Ibrahim Dauda, ya bayyana nadamar sa, inda ya ce daga yanzu ba zai sake satar waya da sayar da kayan shaye-shayen a Kano ba, tunda ya ga ba hanya ce mai ɓullewa ba.
Daga bisani, Kwamandan rundunar tsaron ta Anti-illicit drugs and Phone Snaching force, da akafi sani da KOSSAP, ya ce za su miƙa matashin inda ya dace domin girbar abinda ya shuka.
Ya kuma ce duk wanda suka kama da aikata miyagun ayyuka ko sayar da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya, da faɗan daba ba za su saurara masa ba, ko wane ne, domin ƙara wanzar da zaman lafiya a Kano.



