Majalisun dokoki 25 sun amince da ƙudirin kafa ƴansandan Jihohi a Najeriya.

Majalisun dokokin jihohi 25 a Najeriya, sun amince da ƙudirin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar da ke neman kafa rundunonin ’yansandan jihohi.
Rahotanni sun bayyana cewa, amincewar ta sa ƙudirin ya zarce mafi ƙarancin jihohi 24 da kundin tsarin mulki ya tanada domin yin gyara, bisa sashe na 9(2) na kundin tsarin mulkin 1999.
Jihohin da suka amince da ƙudirin sun haɗa da Ogun, Delta, Plateau, Kwara, Adamawa, Edo, Osun, Oyo, Rivers, Zamfara, Kaduna, Nasarawa, Taraba, Yobe da Kebbi.
Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun amince da ƙudirin a watan Yuni da Yuli na 2026, kafin a miƙa shi ga majalisun dokokin jihohi domin tantancewa.
Ƙudirin na neman sauya tsarin aikin ’yansanda daga jerin ayyukan da gwamnatin tarayya kaɗai ke da ikon tafiyarwa, zuwa tsarin da zai bai wa jihohi damar kafa nasu rundunonin ’yan sanda.
A ƙarƙashin sabon tsarin, rundunar ’yansandan Najeriya za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a jiha har sai rundunar ’yan sandan jihar ta fara aiki.
Haka kuma, rundunar tarayya za ta ci gaba da kula da ayyukan da suka shafi tarayya, tare da taimaka wa rundunonin jihohi a wasu yanayi na musamman, kamar lokacin da matsalar tsaro ta gagari rundunar jihar.
Ana sa ran Majalisar Dokoki ta Ƙasa za ta kammala sauran matakan da suka dace, sannan ta miƙa ƙudirin ga Shugaba Bola Tinubu domin sanya hannu, kamar yadda kafar Daily Nigerian ta ruwaito.
A wani rahoto makamancin haka, ƙungiyar shugaban ƙasa mai kula da sauye-sauyen ’yan sanda ta ce nan ba da jimawa ba za ta miƙa wa Majalisar Dokoki ta Ƙasa ƙudirin dokar aikin ’yan sanda na ƙasa.



