An zargin wata mata da daɓa wa mijin ta wuƙa kan rikicin waya da kuɗi.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wata matar aure mai shekaru 18, Fatima Dalha, bisa zargin daba wa mijinta wuƙa a ciki sakamakon rikici kan waya, kuɗi da zannuwa a Lirr Bajar, Ƙaramar Hukumar Dass.
Wannan na cikin sanarwar da Kakakin Rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar a ranar Lahadi, 25 ga Oktoba, 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa rikicin ya faru da misalin ƙarfe 6:00 na safe, bayan Fatima ta nemi mijinta mai shekaru 30 ya mayar mata da kuɗi, zannuwa da wayar salula da ta yi iƙirarin cewa nata ne.
Takaddamar ta rikide zuwa faɗa, inda ake zargin ta ɗauki wuƙa ta daba masa a ciki, kamar yadda kafar Arewa update ta ruwaito.
Bayan faruwar lamarin, wasu fusatattun mutane sun yi yunƙurin ɗaukar doka a hannunsu kan matar, amma jami’an ’yan sanda daga Dass suka ceto ta. An garzaya da mijin zuwa asibiti, inda yake kwance yana karɓar kulawar likitoci.
Rundunar ta bayyana cewa an tsare matar tare da ƙwato wuƙar da ake zargin an yi amfani da ita. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin ci gaba da bincike, tare da shirin miƙa lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na jihar.



