Rundunar Kossap ta kama matasa 10 bisa zargin sanen wayoyi da kuɗaɗen jama'a a Bata zuwa Ƴan kura da ke Kano.

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba, ƙwacen waya da daƙile sha da dillancin kayan maye, ta Anti-illicit drugs/Phone Snaching force a Kano, ta kama mutane 10, bisa zargin su da yi wa mutane sanen wayoyi da kuɗaɗe a kasuwar Bata zuwa Ƴan Kura.
Kwamandan rundunar tsaron, Nura Salisu Sharaɗa ne ya bayyana kama matasan yayin zantawar sa da Dala FM Kano a Litinin 2 ga watan Nuwamba, 2026.
A cewar sa, "Bayan da rundunar mu ta samu bayanan sirri kan yadda ake yawan Sanen wayoyi da kuɗin jama'a a kasuwar Bata zuwa Ƴan Kura, ne, muka tura jami'an mu na Operation Phone Snaching, ƙarkashin jagorancin Bala Abubakar, a kasuwar da kewaye," in ji shi.
Nura Sharaɗa ya ce da jami'an nasu suka shiga kasuwar ne suka samu nasarar kamo matasa 10 da zargin sane wayoyi da kuɗaɗen matasa a kasuwar.
Ya ce matasan da suka kama sun haɗar da Sani Ibrahim ɗan unguwar Fagge, mai shekaru 27, da Abdullahi Sani mazaunin Rijiyar Lemo, mai shekaru 12, Auwalu Sadik Gyaranya, mai shekaru 23, sai Yusuf Idris mai laƙabin Ɗan Kunne, ɗaj unguwar Burget, mai shekaru 21.
Sauran su ne Nura Adamu mazaunin unguwar Rimin Keɓe, da Aminu Muhammad, Burget Rimin Keɓe, mai shekaru 21, Nura Sani Rimin Keɓe, Sulaiman Shu'aibu mazaunin Kwana huɗu, da Muhammad Yusuf mazaunin Na'ibawa, sai Sadik Garba ɗan unguwar Rimin Keɓe, mai shekaru 25.
Kwamandan rundunar ta Kosssp, Nura Sharaɗa ya kuma ce, abinda ya basu mamaki shi ne yadda matashi guda daga cikin matasan ya gwada musu yadda suke yin sanen, da har ya zare wayar guda daga cikin jami'an su ba tare da sun gani ba a wajen.
Da yake bayyana nadamar sa matashi Sani Ibrahim ya ce, aƙalla sun kai tawaga guda biyar da suke yin sanen waya da kuɗaɗe a yankin Bata da Ƴan Kura, wanda ya ce ya shafe kusan shekaru goma yana sanen waya amma yanzu ya daina.
A cewar sa, ba sa yi wa ƴan kasuwar da ƴan tawagar su sanen waya ko kuɗi, saboda yadda suka san junan su amma dai daga yanzu ya daina sanen.
Abdullahi Naziru Mustapha Yakasai, matashi ne da matasan suka sanewa wayar salula a Ƴan kura, ya ce ya ji daɗi da jami'an suka kamo waɗanda suka sace masa waya tare da ƙwato wayar sa, har aka dawo masa da ita.
Daga bisani rundunar tsaron ta Anti-illicit drugs and Phone Snaching force a Kano, ta gargaɗi masu aikata irin wannan laifi da su daina kasancewar duk wanda ya faɗa komar su ba zai ji da daɗi ba.



