Maukibi: Rundunar Anti-Phone Snaching force ta ba za zaratan jami'an ta don yaƙi da ɓata gari a Kano.

Rundunar tsaro ta Anti Phone Snaching force a nan Kano, ta ce ta ba za zaratan jami'an ta a lungu da saƙo na jihar nan, domin yaƙi da ɓata garin da ke fakewa a cikin masu gudanar da Maukibi suna tada hankalin al'umma.
Kwamandan rundunar a nan Kano, Nura Salisu Sharaɗa ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Dala FM a juma'ar nan, a wani ɓangare na shirin da suka yi na yaƙi da ɓata gari a yayin bikin Maukibi da za a gudanar a ranar Asabar 3 ga Octoba, 2026.
Ya ce ba za su saurara wa dukkan masu sha da dillancin kayan maye, da kuma harkar daba a faɗin jihar Kano ba, a don haka masu aikata wannan laifi su shiga tai tayin su tun kafin su shiga hannun su.
A cewar sa, "A kullum mu na ta faɗa cewa a duk irin wannan lokaci idan ya taso za a yi wani babban taro, ba ma ƙasa a gwiwa wajen baza jami'an mu lungu da saƙo, kuma yanzu ma da za a yi Maukibi, mun baza su," in ji Nura.
Sharaɗa ya kuma ƙara da cewa, tuni ya umarci jami'an sa na Operation Damisa Ƙi Sabo, ƙarkashin jagorancin DC Operation, Abduljalal Sa'idu, domin shiga lungu da saƙo yayin taron Maukibin domin inganta tsaro.
A cewar sa, yanzu haka suna ta tattara bayanan sirri a kan dukkan ɓata gari, kuma duk wanda ya shiga hannun su ba za su ƙyale shi ba, domin ƙara wanzuwar zaman lafiya a faɗin jihar Kano.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya'u ya ruwaito cewa, Nura Sharaɗa ya kuma gargaɗi matasan da ke faɗan daba, da aikata sauran laifuka da su daina kasancewar duk wanda suka kama zai yi dana sani domin ba za su saurara masa ba.



