Koma Labarai
Tsaro

Rundunar ƴan sandan Kano ta jaddada haramcin hawa doki a faɗin jihar

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Rundunar ƴan sandan Kano ta jaddada haramcin hawa doki a faɗin jihar

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sake jaddada haramcin gudanar da hawan daba da hawan dawakai a wuraren taruwar jama’a, tare da gargadin masu shirya irin waɗannan bukukuwa da su bi umarnin.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin ganawar sa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano, a ranar Juma'a 2 ga Octoba, 2026.

A cewar sa, "Gwamnatin jihar Kano ce ta sanya dokar bayan tuntuɓar hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da zaman lafiya da kiyaye doka da oda a jihar," in ji shi.

CP Bakori ya kuma nuna damuwa kan rahotannin da ke nuna cewa, wasu na karya wannan umarni, yana mai cewa har yanzu matsalolin tsaron da suka sa aka sanya dokar suna nan.

Ya ƙara da cewa duk wanda aka samu ya hau dokin ba tare da neman izini ba za a kama shi ko wane ne a jihar, tare da ɗaukar mataki a kan sa.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM