An naɗa Barr. Hafsat Ada'u Kutama a matsayin muƙaddashiyar shugabar Hukumar PCACC.

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa Barr. Hafsat Ada’u Kutama a matsayin mukaddashiyar shugabar Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC.
Barr. Hafsat Kutama ta kasance Sakatare kuma Mai Ba da Shawara kan Harkokin Shari’a na hukumar, matsayinta da Gwamna Yusuf ya naɗa ta a watan Agustan 2025.
Naɗin nata ya zo ne bayan sauyin shugabanci a hukumar, wadda a shekarar 2025 Gwamna Yusuf ya tura sunan Sa'idu Yahya zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano, domin tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar.
A ranar Laraba 16 ga watan Satumba, 2026, ne dai wani labari ya ɓulla, da ke bayyana cewa Sa'idu Yahaya ya yi murabus daga muƙamin shugaban hukumar karɓar korafe-korafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.



