Koma Labarai
Labarai

Majalisa ta buƙaci gwamnatin Kano ta kammala aikin Dam Ɗin Watari da ke Ɓagwai.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Majalisa ta buƙaci gwamnatin Kano ta kammala aikin Dam Ɗin Watari da ke Ɓagwai.

Majalisar Dokokin Kano ta buƙaci gwamnatin jihar da ta tabbatar da an kammala aikin Dam Ɗin Watari da ke ƙaramar hukumar Ɓagwai.

Da yake gabatar da ƙudirin ɗan majalisar da ke wakiltar ƙananan hukumomin Ɓagwai da Shanono, Ali Lawan Alhassan, ya ce an gina dam ɗin a shekarar 1988 domin kamun kifi, dakile ambaliyar ruwa da samar da ruwan sha da ban-ruwa.

Ya ce an bayar da kwangilar faɗaɗa tsarin ban-ruwan a shekarar 2022, tare da tallafin Bankin Raya Ƙasashen Musulmi da gwamnatin Kano, domin samar da ban-ruwa a filayen noma kimanin hekta dubu ɗaya.

Sai dai ya ce an yi watsi da aikin, yayin da kamfanin da ke gudanar da shi ya bar wurin, ya kuma bar ramuka a gonaki, lamarin da ke jefa al’umma cikin haɗari.

Wakilinmu Sunusi Shu'aibu Musa ya ruwaito cewa, Majalisar ta kuma buƙaci a kafa kwamiti domin binciken aikin da yadda aka bayar da kwangilar, tare da gabatar da shawarwarin da suka dace akai.

Ready to PlayDala FM88.5 FM