Koma Labarai
Labarai

Tsadar Fetur: Masu dai-dai ta sahu sun fara matse kafureton baburansu a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Tsadar Fetur: Masu dai-dai ta sahu sun fara matse kafureton  baburansu a Kano.

Yayin da farashin man fetur ke ƙara hauhawa a Najeriya, masu ababen hawa na ci gaba da kokawa kan yadda ƙarin farashin man ke zama alaƙaƙai a gare su.

Yanzu haka dai ana samun farashin kowacce litar fetur ɗaya a kan kuɗi naira 1,460, zuwa 1,430, a wasu sassan jihar Kano, wasu guraren sama da haka, wani gurin kuma ƙasa da hakan.

Da yake zantawa da Dala FM Kano, wani direban baburin dai-dai ta sahu a yankin Sharaɗa Usman Sani, ya ce tashin farashin man na matuƙar ci musu tuwo a ƙwarya.

A cewar sa, "Yanzu haka mu na sayen kowacce litar mai ɗaya a kan kuɗi naira 1,460, 1,450, wasu guraren kuma naira 1,500, a sassan jihar Kano, abin yana damun mu," In ji shi.

Direban adai-daita sahun ya kuma ce, yanzu haka tsadar man ta sanya da yawan masu baburan suna zuwa a matse musu kafureton baburan domin a rage shan mai, saboda halin da suka samu kan su a cikin da tsadar fetur.

A cewar sa, "Ta hanyar rage man ne za mu ɗan samu ɗan na kashewa idan muka yi aiki, domin a yanzu bayan tsadar man ba ma samun fasinjoji yadda ya kamata," In ji shi.

Mutumin ya kuma yi kira ga gwamnati da sauran shugabanni, da su yi duk mai yiyuwa domin ganin farashin fetur ɗin ya sauka don samun sauƙi.

Ready to PlayDala FM88.5 FM