Koma Labarai
Labarai

Shugaban hukumar karɓar korafe-korafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano, Sa'idu Yahaya, ya yi murabus.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Shugaban hukumar karɓar korafe-korafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano, Sa'idu Yahaya, ya yi murabus.

Rahotanni sun bayyana cewa, Shugaban hukumar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) Sa'idu Yahaya, ya yi murabus daga mukaminsa.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa, matakin murabus ɗin ya biyo bayan zargin matsin lamba daga gwamnatin Kano, sakamakon damuwa kan alaƙar siyasa da kuma kusancinsa da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Sai dai har yanzu ba a samu cikakken bayani kan dalilin murabus ɗin ba, yayin da Saidu Yahaya da gwamnatin Jihar Kano ba su tabbatar da rahoton ba.

An naɗa Sa'idu Yahaya a matsayin Shugaban PCACC a watan Agustan 2025, bayan kammala wa’adin tsohon shugaban hukumar, Muhyi Magaji Rimin Gado. Daga bisani Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da nadin nasa na wa’adin shekaru biyar.

Rahoton murabus ɗin ya zo ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen siyasa a Jihar Kano, musamman bayan ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga Jam’iyyar NNPP zuwa Jam’iyyar APC.

Ana sa ran samun karin bayani daga hukumomin da abin ya shafa kan halin da ake ciki.

Ready to PlayDala FM88.5 FM