Koma Labarai
Labarai

Za mu wadata ƙwaryar birnin Kano da ruwan sha nan da watanni 8 - Gwamnatin Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Za mu wadata ƙwaryar birnin Kano da ruwan sha nan da watanni 8 - Gwamnatin Kano

Gwamnatin Kano ta ce nan da watanni takwas masu zuwa ruwan sha zai wadata a fadin ƙwaryar birnin jihar.

Kwamishinan da ke riƙon ma'aikatar ruwan a Kano, kuma kwamishinan ma'aikatar muhalli da sauyin yanayi, Dakta Ɗahir Muhammad Hashim ne ya bayyana hakan, yayin wata ziyarar duba aiki da ya kai, a matattarar ruwa ta Goron dutse, da ke Kano.

Ya ce sakamakon korafe-korafen da al'ummar Kano ke yi na rashin ruwa, ya sa gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf ya tashi tsaye wajan ganin an magance matsalar a faɗin jihar Kano.

Wakilinmu Abubakar Sabo ya ruwaito cewa Dr. Ɗahir ya Kuma ce, akwai matattarar ruwan da an kai shekara talatin ba a zuba mata ruwa ko Lita ɗaya ba a Goron Dutsen, a don haka ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajan ganin an magance matsalar ruwan a ƴan watannin nan.

Idan ba a manta ba dai, tun a kwanakin baya ne gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin ta na gyare-gyare a ɓangaren ruwan wanda zai laƙume sama da biliyan sha ɗaya.

Ready to PlayDala FM88.5 FM