Mamakon ruwan sama ya haifar da ambaliya tare da kashe Kaji a yankin mu - Mazauna Sharaɗa Unguwar Kwari a Kano.

Mamakon ruwan sama ya haifar da ambaliya tare da kashe Kaji a yankin mu - Mazauna Sharaɗa Unguwar Kwari a Kano.
Al'ummar unguwar Sharaɗa gidan Kwari da ke ƙaramar hukumar Kumbotso, sun koka bisa yadda suka ce wasu sun yi gine-gine a kusa da babbar magudanar ruwan su lamarin da ke haifar musu da ambaliyar ruwa.
Mazauna yankin sun ce a duk lokacin da ruwan sama ya fara sauka, ko kuma hadari ya taso, suna matuƙar shiga tashin hankali sakamakon yadda ruwan sama ke shiga cikin gidajen su.
Wani guda daga cikin mazauna unguwar Sharaɗa gidan Kwari, da ke karamar hukumar Kumbotso, Salisu Tukur, ya ce wasu gine-gine da aka yi a babbar hanyar magudanar ruwan yankin ne ke haifar musu da ambaliyar ruwan.
Ya kuma ce ko a ruwan saman da aka yi a cikin daren jiya Talata, ruwan ya shiga gidajen mutane da dama, har ma ta kai ga sai da aka yi aikin ceto mutane daga cikin ruwan a gidajen su.
A cewar sa, "Shigar ruwan saman gidajen mutane ya haifar da mutuwar Kaji, da dama, tare da jiƙa kayayyakin sawar mutane da tabarmi dole sai fito da su aka yi aka shanya su a waje," in ji Salisu.
Ya kuma ƙara da cewa babban burin su shi ne, Gwamnatin Kano, da ma dukkanin masu ruwa da tsaki na yankin, su kai musu ɗauki, domin fitar da su daga matsalar da taa daɗe tana damun su, duba da yadda ambaliyar ruwan ke barazana ga rayuka da dukiyoyin al'ummar yankin.



