Koma Labarai
Labarai

Majalisar dokokin Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin Ɓagwai, Bebeji, Rogo, kan badaƙalar kuɗi a ofisoshin su.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Majalisar dokokin Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin Ɓagwai, Bebeji, Rogo, kan badaƙalar kuɗi a ofisoshin su.

Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin Ɓagwai da Bebeji da kuma Rogo, bayan samun su da badaƙalar kuɗi a ofisoshin su.

Bayan gabatar da rahoton da Kwamitin majalisar na ƙananan hukumomi da masarautu ya yi, ya ce ya karɓi korafe-korafen mutane da wasu daga cikin majalisun kansilolin ƙananan hukumomin kan zarge-zargen da ake yi musu.

Shugabannin ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Alhaji Bello Abdullahi Gadanya na Bagwai, da Dr. Alhassan Salisu na Bebeji, da kuma Alhaji Abubakar Mustapha Rogo, na Rogo.

Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano, Hon. Lawan Husaini Dala, ne ya karanta rahoton a madadin shugaban kwamitin a ranar Talata 4 ga Agusta, 2026.

A dai zaman majalisar na wannan rana, ta amince da dokar bai wa kwalejin Sa'adatu Rimi damar yin Digiri na ɗaya da na biyu ba tare da haɗin gwiwa da wata jami'a ta gida ko ta waje ba.

Wakilinmu Sunusi Shuaib Musa ya ruwaito cewa, mataimakin shugabannin ƙananan hukumomin za su cigaba da jagorantar kananan hukumomin, har sai an kammala bincike.

Ready to PlayDala FM88.5 FM