Koma Labarai
Labarai

Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar ya musanta goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar ya musanta goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027.

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku, ya musanta rahotannin da ke yawo cewa ya bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027.

Wannan na cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Bashir Adefaka, ya fitar a ranar Talata 04 ga Agusta, 2026.

Sarkin Musulmin ya bayyana rahotannin a matsayin ƙarya da yaudara, yana mai jaddada cewa ba shi da ɗan takarar da yake marawa baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Sanarwar ta ce, a matsayinsa na jagoran addini da na gargajiya kuma uba ga dukkan 'yan Najeriya, ba zai iya shiga siyasar jam'iyya ko nuna goyon baya ga wani ɗan takara ba.

Kazalika Sanarwar ta kuma ce Sarkin Musulmin ba shi da wani ɗan takarar da ya fi so, kuma ba zai bayyana goyon bayansa ga kowane mai neman takara ba, a fili ko a ɓoye.

A cewar sa, "Mun lura da wani rahoto da ke yawo a wasu kafafen sada zumunta wanda ke ƙoƙarin nuna cewa Sarkin Musulmi ya buƙaci 'yan Najeriya su goyi bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027,"

Sarkin Musulmin ya ce matsayinsa na buƙatar ya kasance mai adalci da nuna tsaka-tsaki ga kowa, ba tare da la'akari da jam'iyyar siyasa ko ra'ayin siyasar mutum ba.

"Martaninmu a takaice shi ne, ba zai yiwu Sarkin Musulmi, wanda uba ne ga kowa, ya yi irin wannan furuci ba, a bainar jama'a ko a wani wuri," in ji sanarwar.

Ya ƙara da cewa ofishin da yake riƙe da shi ya wajabta masa kasancewa tsaka-tsaki, don haka bai dace ya marawa wani ɗan takara baya kafin gudanar da zaɓen ƙasa ba, kamar yadda kafar Daily Nigerian ta ruwaito.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa masu alaƙanta Sarkin Musulmin da yaƙin neman zaɓen Tinubu na 2027 na ƙoƙarin jefa shi cikin siyasar jam'iyya domin cimma muradunsu na kashin kai.

Ready to PlayDala FM88.5 FM