Rikicin masarauta: ku gujewa tinzira matasa ba mu da in da ya fi Kano - Sheikh Ali Ɗanabba

Kwamishina na biyu a Hukumar Shari'a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗanabba, ya buƙaci wasu manya da ke bayyana kalaman tunzuri a jihar nan da su daina, domin gujewa tashin hankali a faɗin jihar.
Sheikh Ali Ɗanabba ya bayyana hakan ne a yayin huɗubar juma'ar da ya gabatar a masallacin Hukumar Shari'a ta jihar Kano, a ranar Juma'a 2 ga watan Oktoba, 2026, mai taken "Ka da ku jangwalo mana fitina".
A cewar malamin matsalar da ake samu ta Masarautar Kano, bai kamata rinƙa samun ta ba, duba da yadda jihar ke zaune lafiya.
Wannan na zuwa ne biyo bayan yadda ake ci gaba da samun wasu maganganu daga ɓangaren wasu manyan mutane da suke da jiɓi da masarauta a jihar, wanda kalaman nasu kan iya tunzura matasa da hakan ka iya haifar da matsala.
A cewar Sheikh Ɗanabba, bai kamata a rinƙa samun wasu manya na bayyana kalaman da ka iya kawo matsalar tsaro a jihar Kano ba.
"Masu waɗannan kalaman a kan rikicin masarautar, kamata ya yi su rinƙa tunawa da ƙissar Annabi Yusuf A.S, wanda duk abubuwan da ya fuskanta amma da ya yi haƙuri gashi nan har Sarki ya zama," in ji Ɗanabba.
Ya kuma ƙara da cewa, ba dai-dai ba ne a rinƙa samun manya na bayyana kalaman da za su hargitsa jihar Kano da kuma matasa ba, kasancewar suna da daraja kamata ya yi su ka bakin su, su yi shiru.
Sheikh Ɗanabba ya kuma ce, akwai buƙatar mutane su rinƙa tunawa da mutuwa, domin yanzu ne ana tare da mutum amma anjima kaɗa ya koma ga Ubangiji S.W.T.
Malamin ya kuma buƙaci iyaye da su ja hankalin ƴaƴan su, domin gujewa barin yin amfani da su wajen tada fitina a faɗin jihar Kano.
Ya kuma gargaɗi matasa da su gujewa barin yin amfani da su wajen tada hankalin al'umma, mai-makon hakan ya fi dacewa su yi abinda ya kamace su.
A cewar sa, "matsalolin da ake fuskanta a jihar, in da za a kai ta Hukumar Shari'a ta jihar Kano, sai ta zo ƙarshe, domin akwai hanyoyin da suke bi wajen warware su," in ji Ɗanabba.
Malamin ya kuma buƙaci shugabanni da su ƙara sanya haƙuri a zukatan su, tare da miƙa wa Allah S.W.T, komai domin samun mafita a dukkanin lamuran su.



