Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta gayyaci mawaki Tijjani Gandu kan wata waƙa da ya yi.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta gayyaci fitaccen mawakin siyasa Tijjani Gandu, bisa zargin sakin wata waƙa ba tare da gabatar da ita domin tantancewa ba.
Wannan na cikin wata sanarwa da jami'in yaɗa labaran hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a madadin shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, a ranar Asabar 3 ga watan Oktoba 2026.
Sanarwar ta ce, hukumar ta bayyana cewa dokarta ta buƙaci mawaƙa da marubuta da su rinƙa gabatar da ayyukansu kafin sakin su ga jama’a, kamar yadda kafar DCL Hausa ta ruwaito.
Hukumar ta kuma gargaɗin cewa ƙin amsa gayyatar mawaƙin na iya sawa ta ɗauki matakan da doka ta tanadar.



