Ku guji duk abun da zai haifar da rikici, fitina ko rarrabuwar kai - Sheikh Ali Ɗanabba

Kwamishina na biyu a Hukumar Shari'a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗan Abba, ya bayyana kwanciyar hankali a matsayin babban ginshiƙin zaman lafiya da ci gaban al’umma a kowane fanni na rayuwa.
Sheikh Ali Danabba, ya bayyana hakan ne a yayin gabatar da Hudubar Juma’a mai taken “Kada Ku Jangwalo Mana Fitina”, a Masallacin Juma’a na Hukumar Shari’a da ke Kano.
Sheikh Ali Danabba ya ce zaman lafiya na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ci gaban al’umma, da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Malamin ya kuma yi kira ga al’umma da su guji duk wani abu da ka iya haifar da rikici, fitina ko rarrabuwar kai, yana mai jaddada cewa addinin Musulunci ya koyar da zaman lafiya, haƙuri da mutunta juna.
Ya kuma buƙaci jama’a da su rinƙa warware matsaloli cikin lumana, tare da gujewa kalamai ko ayyukan da ka iya haifar da tashin hankali.
Sheikh Ali Ɗanabba ya jaddada cewa tabbatar da zaman lafiya ba nauyin gwamnati da jami’an tsaro kaɗai ba ne, illa nauyi ne da ya rataya a kan kowane ɗan adam.
Ya ƙara da cewa haɗin kai, fahimtar juna da bin doka su ne wasu daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen gina al’umma mai zaman lafiya da ci gaba.
A ƙarshe, Malamin ya yi kira ga al'ummar Musulmai da sauran al’umma, da su ba da muhimmanci ga zaman lafiya, tare da guje wa duk wani abu da zai iya haddasa fitina da rarrabuwar kai.



