Koma Labarai
Iftila'i

Jami'in hukumar Karota, ya samu karaya shida a jikin sa, bayan wani mai mota ya buge shi a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Jami'in hukumar Karota, ya samu karaya shida a jikin sa, bayan wani mai mota ya buge shi a Kano.

Hukumar Kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta bayyana cewa jami'in ta mai suna Nasiru Abdullahi, wanda aka fi sani da Baba Nasiru, ya gamu da iftila’i bayan wata mota ta buge shi a kan titin Dambatta.

Hukumar ta ce lamarin ya jawo wa ɗan karotan samun karaya guda shida a sassa daban-daban na jikinsa.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa, wannan na cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban hukumar Karota, a shafukan sada zumunta, Mu’azzam Mansur Kurawa, ya fitar a ranar Lahadi 23 ga Agusta, 2026.

Sanarwar ta bayan faruwar lamarin ne mai motar ya gudu daga wurin, inda jami’an ‘yan sanda suka bi sawunsa, amma ba su samu nasarar kama shi ba.

Sanarwar ta kuma ce jami’in na samun kulawa a sashen bada agajin gaggawa na Asibitin Murtala Muhammad da ke birnin Kano.

"A lokacin da aka kawo jami'in asibitin, babu gado da zai kwanta, sai dai da zuwan Manajan Daraktan hukumar KAROTA, Injiniya Faisal Mahmud Kabir, ya shiga cikin lamarin da kansa tare da neman a samar da gado domin jami’in ya samu damar kwanciya da ci gaba da samun ingantacciyar kulawar lafiya," in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma ce wannan mataki ya sake bayyana irin kyakkyawan shugabanci da kulawar Injiniya Faisal Mahmud Kabir ke bai wa jami’an hukumar, tare da tabbatar da cewa walwala da lafiyar ma’aikata na daga cikin abubuwan da yake bai wa muhimmanci.

Hukumar ta kuma yi addu'ar Allah ya bai wa jami’in cikakkiyar lafiya, ya saukaka masa, ya kuma dawo da shi bakin aiki cikin koshin lafiya.

Ready to PlayDala FM88.5 FM