’Yan mata uku ƴan gida ɗaya sun rasu sakamakon kifewar kwale-kwale a Dam ɗin Tiga, Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa, ƴan mata uku ƴan gida ɗaya, daga garin Yalwan Rugu-Rugu da ke Karamar Hukumar Tudunwada a Kano, sun rasu sakamakon kifewar kwale-kwale a Dam ɗin Tiga da ke jihar.
Hakan na cikin sanarwar da Shugabar Karamar Hukumar Tudunwada, kuma shugabar shugabannin ƙananan hukumomin Kano (Algon Chairman) Hajiya Sa’adatu Salisu Soja Maijama’a ta fitar ga manema labarai.
Sanarwar ta ce, bayanai daga ’yan uwan mamatan sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na ranar Asabar 29 ga watan Agustan 2026, inda kwale-kwalen da ’yan matan suke ciki ya kife a Dam ɗin Tiga.
Waɗanda suka rasu sun haɗar da Murjanatu, da Atikatu da Bilkisu wadda ake kira Amira, dukkanin su ƴan gida ɗaya.
Kafar Arewa updates ta ruwaito cewa, Shugabar Karamar Hukumar ta Tudun wada, ta kuma yi ta’aziyya ga iyalan mamatan da al’ummar yankin tare da yi wa ’yan matan addu’ar Allah ya jiƙansu da rahama.



