Almajirai 4 sun rasu bayan cin wani Kifi mai ɗauke da maganin Ɓera a Kano.

Aƙalla Almajirai huɗu na Tsangayar Malam Iliyasu Mai Tsangaya da ke Kadage Sharifai a Ƙaramar Hukumar Ungogo, sun rasu bayan cin wani Kifi mai ɗauke da maganin Ɓera.
Shugaban ƙungiyar Tsangaya Media Network ta ƙasa, Alaramma Sani Musa Nuhu, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Litinin 17 ga watan Agusta, 2026.
Sanarwar ta ce, almajiran sun rasu ne a Asibitin Malam Aminu Kano a daren Lahadi, 16 ga Agusta, 2026, bayan sun ci abincin da ake zargin ya gurɓata.
An yi zargin cewa abincin da almajiran suka ci na ɗauke da wani Kifi wanda aka sanya wa maganin Ɓera, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar su.
Kafar yaɗa labarai ta Arewa updates ta ruwaito cewa, Sanarwar ta ƙara da cewa, an gudanar da jana’izar almajiran bayan samun umarni daga Dagaci da baturen ƴan sandan yankin.



