Koma Labarai
Iftila'i

Matashi Abdullahi Aminu ya rasu sakamakon faɗawa kududdufi a Ɗanbatta da ke Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Matashi Abdullahi Aminu ya rasu sakamakon faɗawa kududdufi a Ɗanbatta da ke Kano.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar wani matashi mai suna Abdullahi Aminu, sakamakon faɗawa cikin kududdufi a Ƙofar Gabas da ke ƙaramar hukumar Ɗanbatta.

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aiko wa Dala FM Kano, a ranar Laraba 12 ga watan Agusta, 2026.

Ya ce a ranar Talata 11 ga watan Agustan 2026, sashen karɓar kiran gaggawa na hukumar da ke ƙaramar hukumar Ɗanbatta, ya karɓi kiran gaggawa daga wajen Aminu Lawan, wanda ya sanar da faɗawar ɗan sa a cikin kududdufi da ke yankin.

A cewar sa, "Da isar jami'an mu suka shiga cikin kududdufin domin ceto rayuwar yaron mai suna Abdullahi Aminu ɗan shekaru 18, sai dai sun ciro shi baya cikin hayyacin sa, inda daga bisani aka tabbatar da rasuwar sa," in ji Saminu.

Ya kuma ce daga bisani ne jami'an hukumar suka miƙa gawar matashin zuwa wajen Sakataren Hakimin Ɗanbatta, Alhaji Baba Ado, Sarkin Bai, domin a yi masa sitira kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Hukumar ta kuma miƙa saƙon ta'aziyyar ta da jajanta wa, ga ƴan uwan Marigayin da ya rasa ransa sanadiyyar faɗawa cikin kududdufin a Ƙofar Gabas da ke ƙaramar hukumar Ɗanbatta.

Ka zalika, hukumar kashe gobarar ta jihar Kano, ta kuma gargaɗin al'umma da su kaucewa barin yara su kusanci kududdufi, ko cikin Dama-damai, da sauran su, domin gujewa faruwar irin wannan Iftila'in a nan gaba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM