Wasu ɓata gari sun yi wa matashi Saifullahi yankan rago a Kano

Wasu ɓata gari sun yi wa matashi Saifullahi mai shekaru 29, ɗan garin Gora da ke ƙaramar hukumar Madobi a Kano, yankan Rago, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar sa.
Ɗan uwa ga matashin, kuma Shugaban Gamayyar Matasan Kano, Muhammad Tijjani Ɗorayi (MTD) ne ya tabbatarwa Dala FM Kano, hakan a ranar Lahadi 11 ga watan Oktoba, 2026.
A cewar sa, ɓata garin sun yi wa matashin yankan rago ne a lokacin da yake kan hanyar sa ta komawa gida daga cikin gari cikin dare, inda suka buƙaci ya rage musu hanya, daga bisani suka yi masa aika-aikar.
MTD ya ce lamarin ya faru a cikin daren jiya Asabar 10 ga Octoba, 2026, inda bayan faruwar lamarin waɗanda ake zargi da kisan suka kira ta wayar sa suka sanar da abinda suka yi masa.
Ya ce, mutanen sun ce sun buga masa abu ne a kan sa daga bisani suka yi masa yankan rago, suka tafi da baburan sa da kuma wayar sa.
Ya ce matashin mutum ne mai kirki da girmama na gaba da shi tare da yin abinda ya kamace shi.
Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su yi abinda ya kamata domin ganin an zaƙulo waɗanda suka aikata mummunan kisan gillar ga matashin.
Muhammad Tijjani, ya kuka yi addu'ar Allah ya jiƙan Marigayin ya gafarta masa.



