Koma Labarai
Shari'a

Mun bi umarnin kotu wajen danƙawa Mercy Tarfa yara marayu, su kuma sun zaɓi zama a hannun gwamnatin Kano - Kwamishin shari'a

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Mun bi umarnin kotu wajen danƙawa Mercy Tarfa yara marayu, su kuma sun zaɓi zama a hannun gwamnatin Kano - Kwamishin shari'a

Gwamnatin jahar Kano ta bayyana cewar ta danƙa wasu yara a hannun wata mata mai suna Mercy Tarfa, wadda kotu ta ayyana cewar a mayar mata da su sai dai yaran sun turje akan cewar ba za su koma hannun matar ba.

Kwamishinan shari'a na jahar Kano Barrister Abdulkarim Maude SAN, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da manema labarai a ranar Laraba 15 ga Afrilu, 2026.

Ya ce doka ta baiwa duk wani ɗan ƙasa wanda ya haura shekaru 18 damar zaɓar addini da wajen zama, wanda kuma bai kai wannan shekaru ba dokar ƙananun yara ta bashi kariya akan ya zaɓi wajen zama domin daidaita rayuwarsa.

Ma'aikatar shari'a da haɗin gwiwar ma'aikatar mata sun danƙa waɗannan yara ga waccan mata, sai dai yaran sun garzaya a guje wajen kwamishiniyar mata inda suka ce suna jin daɗin zama a ƙarƙashin gwamnatin jahar, kasancewar sun canza addini ba tare da tursasa wa ba idan sun koma wajen Tarfa za su samu tasgaro.

A gefe guda kuma, shugaban ƙungiyar lauyoyi musulmi reshen jahar Kano, (MULAN) Barrister Sanusi Lawan Fandubu, ya ce ƙungiyar su a shirye take ta kare bukatun waɗannan yara.

Ready to PlayDala FM88.5 FM