Mun rabawa marayu kuɗi sama da miliyan 600 na gadonsu a cikin wata ɗaya - Babbar kotun musulunci a Kano

Babbar kotun ɗaukaka ƙara ta shari'ar muslunci a jihar kano ta bayyana cewar kotunan shari'ar musulunci sun yi rabon gado na kuɗi sama da miliyan 600 a ƙasa da wata ɗaya.
Daraktan yaɗa labarai da kididdiga na hukumar ladaftar da ma'aikatan kotunan shari'ar muslunci Muzambil Ado Fagge ne ya bayyana hakan ga gidan rediyon Dala FM Kano, a ranar Laraba 15 ga watan Afrilu, 2026.
Muzambil Fagge ya bayyana cewar an kawo sabbin tsare-tsare ƙarƙashin jagoran Alkalin alkalai Dr. Tijjani Yusuf Yakasai, da babban magatakaddar kotunan shari'ar muslunci Dr. Abubakar Haruna Khalil.
A cewar sa, "Akwai asusun bai ɗaya na kotun ɗaukaka ƙara ta shari'ar muslunci wanda a wannan asusu ne ake sanya kuɗin da zarar kotu ta kammala rabon gadon sai a turawa magada kudin su ta banki, in ji Muzambil."
Ya kuma bayyana cewar akwai umarni daga ofishin babban magatakaddar a kan cewa haramun ne a ajiye kuɗin magada a kotu, ko wani ma'aikacin kotu ya bayar da asusun sa don a sanya kuɗin magada a ciki.
Ya ci gaba da cewa a na biyan kuɗin magada ne daga shelkwatar babbar kotun ɗaukaka ƙara ta shari'ar muslunci, kuma wajibi ne duk wani kudi na magada a sanya su a wancan asusu na bai ɗaya domin gujewa wani abu daban.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, Muzammil ya kuma cewa akwai kuma tsari na alkinta kuɗaɗen marayu ga mai bukata ta hanyar saya musu gidaje a hukumance, don kaucewa danne haƙƙin marayu daga makusanta.



