Koma Labarai
Shari'a

Babu wata kotu da ta wanke Murtala Sule Garko daga zargin badaƙalar kudi - Baba Jibo

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Babu wata kotu da ta wanke Murtala Sule Garko daga zargin badaƙalar kudi - Baba Jibo

Babbar kotun jahar Kano ta musanta jita-jitar da ake yaɗawa kan cewar ta wanke Hon. murtala Sule Garo, daga zargin badaƙalar kuɗi da gwamnatin Kano ta ke tuhumar sa.

Mai magana da yawun babbar kotun Baba jibo Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il, a ranar Talata 14 ga Afrilu, 2026.

A cewar sa, wannan batu ba gaskiya ba ne, kuma babu wata kotu a jahar Kano da ta kori wannan shari'ar da ake yi masa.

"A Shekarar 2025, ne dai gwamnatin Kano ta yi ƙarar Murtala Sule Garo a gaban mai shari'a Sanusi Ado Ma'aji, a kan tuhumar badaƙalar kuɗi, sai dai tun a lokacin lauyoyin Garo sun yi suka akan hurumin kotun, in ji shi."

Ya ci gaba da cewa, a lokacin lauyoyin sun bayyana cewar masu bincike ba su gabatar da wasu kwararan hujjoji akan binciken su ba, a don haka ne ma lauyoyin Garo suka yi suka.

Baba jibo ya bayyana cewar tun a baya babbar kotun jahar ta sallami wanda ake ƙarar, tare da umarnin a je a yi sahihin bincike daga baya kuma hukumar ta gurfanar da shi a wata kotu bayan tayi cikakken bincike.

Har ila yau, Jibo ya bayyana cewar tun a yanzu akwai shari'ar Murtala a gaban babbar kotu kuma babu wata kotu da sallami wannan shari'a, har ma ya ce kotunan da suke irin wannan shari'ar yanzu haka suna hutu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM